7 Maris 2015 - 12:02
Milloli da Aqeedu na 2

Na Shaikh Hamzah Muhammad Lawal MAUDU’IN ILIMIN AL-MILAL WAN-NIHAL

Muna bayani ne akan maudu’in Al-milal wan-nihal, inda muke cewa maudu’in Al-milal wan-nihal shine Aqidu na dukkan ma’abota Aqidun kuma akan haka ne aka rubuta littafai masu yawan gasken gaske,wasu littafan suna magana akan Aqidu A’ammu wato Aqidun na musulunci ne ko bana musulunci ba,a lura da kyau, ba addinai nace ba Aqidu nake nufi.Wasu malaman sun yi bincike akan Aqidun da suke na musulunci kawai,sannan wasu kuma sun yi bincike akan Aqidun makaranta guda daya kawai, koda a cikin musuluncin ne kamar Aqidun Asha’ira masalan. Kenan maudu’in shine Aqidu.Mu a nan kuma muna so mu kebanta da Aqidun Shi’ah tunda mun ce Al- jami’ul kulliy shine maudu’in kowanne ilimi ilimi,kenan ko da a ce mun yi bahasi akan wasu mas’aloli daga cikin masa’il na shi’anci wadanda basu da dangantaka da Aqida to duk gabaki daya makomarsu zuwa ga Aqida ne.Kenan Umdaa a asalin abinda muke so muyi bincike a nan wurin shine Aqidun Shi’ah koda munyi magana akan sauran ababe a cikin Shi’ah,kamar misali;- Me yasa Yan shi’ah basa rike hannayensu acikin sallah? Me yasa Yan shi’ah suka dauka cewa Basmala bangare ce ta kowace sura acikin sallah? Me yasa Yan shi’ah basa karanta juzu’in surah saidai surah cikakka a cikin sallan farilla? Me yasa Yan shi’ah suke yin dabe akan kabari maimakon tulluwa ko kunya da ake yi a nan yankin ? Me yasa Yan shi’ah? me yasa yan shi’ah?mas’aloli na Fiqhu.Duka jawabin me yasa din nan yana komawa ne zuwa ga Aqidunsu su yan shi’ah din ne saboda haka wannan yana daga cikin ababen da zamu yi bincike a asasin Aqidun Yan shi’ah. Dab’an yau Jumu’a sha bakwai ga watan Janairu dubu biyu da sha hudu, kila kuma ya dace da sha bakwai ko sha shida ga watan Rabi’ul Auwal Hijra dubu daya da dari hudu da talatin da biyar. Wannan abinda muke so mu yi yana da fadin gasken gaske.Ina da surah na bahasin gaba daya da kuma masdarori da marajii da bayanai da sharhohi da muke so mu yi akan su. Amma banda surah na iyakan mudda wanda wannan bahasin zai dauka saboda haka ina tsakanin tsoro guda biyu tun lokacin da na fara tunanin in yi bahasin.A gefe daya ina cikin tsoro na tsawon yalwatawa kamar a daya gefen kuma nake cikin tsoran gajartawar kuntatawa,wato ban sani ba in yalwata binciken ya zama ya dauki lokaci mai tsawo? Ko kuma in kuntata binciken sai ya zama ya dauki lokaci gajere?ko ko ALA HADDUL WASAD wato ba wannan ba,ba wancan ba shi yafi?Saboda shi in ka kuntata da yawa din ba dole bane ya zama manufofi sun baiyana gabaki daya,sannan inka yalwata da yawa kila mutane su ga karshen inane ake so a je ba musamman saboda yawancin mutane suna da Adifa sosai su suna so ka je masu kawai SULBUL MAU’DUU wato ka je masu tsakiyan mau’du’in ka dakko mas’aloli wadanda suke an fi sabawa a cikinsu,ya zama cewa kayi magana musamman kuma suna so ya zama cewa kayi masu da lahajojin su da sauran mutane.Ala kulli halin mun haddade mau’du’in. FA’IDOJIN MAUDU’IN AL-MILAL WA-NIHAL Sai mu ce to bincike akan Al-milal wan-nihal yana da fa’ida ko bai da?wato mece ce fa’idan wannan binciken da mu ke so mu yi na Aqidu,musamman kuma Aqidun shi’a?.Sai mu ce;- Ee,yana da fa’ida,bama fa’ida kawai ba yana da fa’idoji masu yawan gasken gaske wadanda zamu iya ambaton wasu daga cikin su kamar haka;- FA’IDA TA DAYA(1) Na farko akwai abin da ake cema AT-TASBEET wato kenan karfafawa da tallafawa da kuma tabbatarwa da ma’abota ita Aqidan din ta hanyar warware masu Aqidunsu da kuma kawo hujjoji da dalilai akan ita Aqidan tasu domin ya zama suna akan basira da gasgata al’amarin su.Ya zama cewa ba suna Intima’i ko karkata ga ita Aqidan bane domin yayi ko domin sun ga wasu suna yi ko wani wan su na yi ko abokin su amma su basu san me suke yi ba, suna yi ne a makance.Wadannan bincike binciken da za mu yi muna fatan insha Allah su zama mabudi da kuma asasi na karfafa ma ma’abota Aqidan wato Yan shi’ah,wannan shine abu na farko musamman tunda muna so mu yi bincike ne mai yalwa kuma ya zamo wani irin bincike ne wanda yake ILMI ACADEMY MUTASALSIL RIYADIY wato akan asasin arithmetic progression ko da bai tafi akan asasin geometric progression ba,ma’ana binciken mu na so mu yi ne a ilmance ta sigan bahasi sannan ya zama daki daki.Bahasin da zai zo a gaba ya zama yana da dangantaka da na baya wato su zama Mutasalsil Riyadiy,da na ce akan asasin lissafin arithmetic progression wato ina nufin za mu dinga addition ne ba multiplication ba maimakon mu dinga multiplying sai mu dinga adition saboda kada ya zama muna sauri a bahasin.Saboda haka fa’ida ta farko itace TASBEET wato kafa hujja kamar yanda Allah{T} yake cewa lokacin da aka kawo ishkal akan Manzon Allah {SAW}a suratul Furqan inda Allah{T} yake cewa;- ﻭَﻗَﺎﻝَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻟَﻮْﻟَﺎ ﻧُﺰِّﻝَ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁَﻥُ ﺟُﻤْﻠَﺔً ﻭَﺍﺣِﺪَﺓً ﻛَﺬَﻟِﻚَ ﻟِﻨُﺜَﺒِّﺖَ ﺑِﻪِ ﻓُﺆَﺍﺩَﻙَ ﻭَﺭَﺗَّﻠْﻨَﺎﻩُ ﺗَﺮْﺗِﻴﻠًﺎ32 To sai Allah{T} yake cewa ;….haka din ya faru ne saboda mu karfafa zuciyarka ya kai Manzon Allah {SAAW}wato don mu karfafi zuciyarka mutallafe ta.Wannan itace fa’ida ta farko kenan. FA’IDA TA BIYU(2) Fa’ida ta biyu itace bada fursa da kuma dama ga mutumin da yake ba Imamiyah yake yi ba ya saurara domin ya ji aqidun shi’ah daga mabubbuga wadda take amintata daga wurin yan shi’a wadanda suka yi karatu a wurin Malaman shi’ah,shukran la fakran ina so a nan in ce na yi karatu daidai gwargwado a wurin Hujjoji da Ayoyin Allah a cikin Aqidan shi’ah wannan zai iya Ahhalani ya bani dama ya zama ina magana da suldani akan shi’anci akan asasin abin da nake hikaitowa daga wadannan Hujjoji da Ayoyin Allah din wadanda da yawa yawan su suna da rai a yanzu saboda haka idan kana so ka san shi’ah alhalin kai ba dan shi’ah bane to wannan silsilan bahasin za taimaka yayi amfani amma da sharuddan da zan ambata insha Allahu a gaba in na zo ina so in yi magana akan sharuddan muhawara saboda muhawara tana da sharudda masu yawan gasken gaske wadanda in daya daga cikin wadannan sharuddan ya rushe to gaba daya muhawara ba ta da amfani saboda haka duk wadannan shimfida ne ba mu shiga cikin bahasin ba.Sannan bayan mun fadi sharuddan muhawara zamu fadi manhaj din da zamu bi a bahasin namu,wannan kuma shine muke nufi da Ilmi Acadeemiy saboda akwai abin da ake ce ma muhawara da akwai kuma abin da ake ce ma Munazarah,sannan akwai abin da ake ce ma Mujadala wanda kuma kowanne yana da ma’anar shi.To lokacin da mu ka zo za mu yi bayani akan sharuddan muhawara zan yi bayani akan wannan nuqda ta biyu.Ala kulli hal fa’ida ta biyu itace cewa wannan wata dama ce ga mutumin da yake da zuciya kubutatta wanda yake so ya fahimci shi’anci.Sabani a cikin yan Adam wannan la budda minhu ne wato dole ne a ringa samun sabani domin dan Adam tun lokacin da aka halicce shi har zuwa lokacin da Allah zai gaji kasa da wanda yake akan ta haka dan adam zai kasance yana sabawa.Annabawa ma an aiko su ne saboda warware sabani saboda haka mutane suna sabawa tun farkon al’ummar musulmi an saba,sahabbai ma akan kansu sun saba, Abubakar da Umar sun saba kamar yadda yake a cikin Sahihul Bukari kila zamu gani wata rana,sannan sahabbai sun saba da Manzon Allah{saw} wanda muke ganin bai kamace su su saba da shi ba,kuma shima ya fadi haka.Amma duk da haka sabani ya faru. Saboda haka sabani wani abu ne daya lizimci dan Adam amma yafi kamata ya zama cewa muna bincike ne akan mas’aloli a lokacin da muka samu Iktilaf ba lokacin da muka samu Kilaf kawai ba,wato har a lokacin da muke da bambamci ba a lokacin da muka saba kawai ba,mutane sun dauka kullun dole ne ya zama ana muhawara in aka saba,a’a, ana yin muhawara ma har a lokacin da ake da bambamci ina so in fahimci ra’ayin ka kuma akwai muhawarori masu yawan gasken gaske a cikin Al’qur ani wanda Allah{T} ya hikaito,alal hakika ma Alkur’ani ya hikaito ko ya yalwata ma’anar Hiwar inda ya fitar dashi daga da’iran Jidal ya shigar dashi da’iran tattaunawa. Tattaunawa ma Alkur’ani ya kira ta muhawara saboda haka wanan itace fa’ida ta biyu. Ita fa’ida ta biyu itace ba wanda yake so ya fahimci shi’anci dama akan ya karanta ya gani yanda shi’anci yake daga Malaman shi’a.Kuma anan muna so mu ce in mutum yana so yayi bincike akan Aqidun da bata shi ba to abu biyu yake bukata:- 1,Na farko shine ya dinka bibiyan wadanda ake ce ma A’alam na wannan Aqidan. 2,Na biyu kuma ya dinga bibiyan abinda yake mashhur. Wannan sharudda ne masu tsadan gasken gaske wadanda kila a gaba zan yi bayanin wadannan kalmomin guda biyu kuma bawai shi’ah kawai ba, kowace aqida aqida in kana so kayi bincike akanta, to ka nemi Ummuhatul kutub na ita wannan aqidan sannan kaji daga A’alam din aqidan sai kuma ka dauki abin da yake Mashhur ba abin da yake Shaaz ba(wato bako)cikin aqidan saboda kowace Aqida tana da manya manyan littafai wadanda suke sune maraajiih wato makoma na ita wannan makarantan ko Aqidah sanan kuma ya hada da jin sharhin da malaman makarantar suka yi a wannan makarantar.kada mutum yazo da kaifiyan shi yace zai fahimce ta da kanshi wannan zan kara bayani kila a gaba.ABNA